BBC navigation

Kanar Dasuki ya kai ziyara Damaturu da Maiduguri

An sabunta: 29 ga Yuni, 2012 - An wallafa a 07:33 GMT
Kanar Sambo Dasuki

Kanal Sambo Dasuki mai ritaya

Sabon mai baiwa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, ya kai ziyara biranen Maiduguri da Damaturu, inda ya nemi da a zauna lafiya.

Biranen Damaturu da Maiduguri dai sun sha fama da tashe-tashen hankula wadanda ke yin sanadiyyar asarar rayuka da jikkatar mutane da dama, kuma wani korafi da al'ummomin wannan yanki suke yi shi ne yadda suka nuna cewa shugabanni sun yi watsi da su.

Wannan ziyarar ita ce ta farko da Kanar Sambo Dasuki yake kaiwa tun bayan hawansa wannan mukami, bayan tsige Janar Andrew Azazi da Shugaba Jonathan ya yi a kwanakin baya.

Mai baiwa gwamnan jihar Yobe shawara a kan harkokin watsa labarai Abdullahi Bego ya ce fatan Kanar Sambo Dasuki shi ne a kawo karshen tashe-tashen hankula kafin fara azumin watan Ramadhana.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.