Ana taro a kan kasashen Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabannin kasashen Turai

A ranar Alhamis ne shugabannin kasashen Turai za su gana a Brussels, babban birnin Belgium a yunkurinsu na warware matsalolin da ke fuskantar tattalin arzikinsu.

Za a yi taron ne duk da cewa Jamus da Faransa ba su warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu ba.

Amma wasu bayanai na nuna cewa kasashen biyu na kara samun fahimtar juna game da yadda za a bullowa matsalar tattalin arzikin yankin.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce suna fatan cimma matsaya a kan manufar kara daidaita tattalin arziki da siyasar kasashen Turai.

Merkel ta ce babu wata hanya mai sauki da za a bi wajen fita daga kangin tattalin arzikin da Turai ke ciki, don haka a cewarta, bai kamata kasashen su rika yin alkawuran da ba za su cika game da batun ba.

Ta kara da cewa dole ne kasashen da ke amfani da kudin Euro su dauki kwararan matakai a fannin siyasa da tattalin arzikinsu kafin su fara tunanin shawo kan matsalolin bashin da suka addabe su.

Shi ma shugaban Faransa, Francoise Hollande, ya bayyana fatan kara dankon alakar da ke tsakanin kasashen.

Shi kuwa shugaban Majalisar kasashen Turai, Herman Van Rompuy, ya ce yana fatan Majalisar ta kara samun karfin iko a kan dokokin banki da na kasafin kudin kasashen Turai.

Karin bayani