Syria: An amince da kafa gwamnatin wucin gadi —Annan

Kofi Annan da Sergei Lavrov Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kofi Annan yana kus-kus da Sergei Lavrov

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman ga Syria, Kofi Annan, ya ce manyan kasashen duniya sun amince da wani shiri na kafa gwamnatin wucin-gadi wadda za ta samar da zaman lafiya a kasar ta Syria.

“Sun shaida min cewa suna goyon bayan shiri na na samar da zaman lafiya, kuma a watan Afrilu kansu ya hadu—lokacin da suka amince da wadansu kudurori guda biyu, amma ina kalubalantarsu su kara kaimi; ina ganin kuma mun dauki hanyar hakan”.

A cewar Amerika manufar shirin ita ce kafa gwamnatin da ba Shugaba Bashar al-Assad a cikinta, amma Rasha ta yi watsi da wannan ikirari, tana cewa ba a gindaya sharadi a kan wanda zai kasansce a cikin gwamnatin rikon kwaryar ba.

Wakilin BBC a wurin taron a Geneva y ace har yanzu akwai rarrabuwar kawuna a tsakanin manyan kasashen a kan matakan da ya kamata a dauka a kan Syria.

A halin da ake ciki kuma, masu fafutuka a kasar ta Syria sun ce sojojin gwamnati sun sake kwace garin Douma wanda ke kusa da babban birnin kasar, wato Damascus, bayan kwashe kwanaki ana yi masa kawanya da luguden wuta.

A cewarsu mutane da dama sun rasa rayukansu yayinda daruruwa suka jikkata, har ma ana ganin gawarwaki a kan titunan garin.

Masu fafutukar sun ce an tilastawa mutane da dama tserewa daga garin yayinda aka rutsa da wadansu—ga shi kuma abinci da ruwan sha sun tasamma karewa.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin kasar ta Syria ya ce sojojin na ci gaba da fatattakar wadanda ya kira 'yan ta'adda a Douma.