Sabon shugaban Misra na gab da rantsuwar kama aiki

Mohammed Mursi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mohammed Mursi

Kasar Masar na shirye shiryen rantsar da sabon zababben shugaban kasar Mohammed Mursi na kungiyar yan uwa Musulmi.

Shi ne zai zamanto shugaban Musuluncin kasar na farko, kuma shugaba na farko da ba tsohon soja ba ne.

To sai dai babban kalubale gare shi, shi ne daidaita harkokin mulki alhali yawancin iko na hannun dakarun sojin kasar.

Mohamed Mursi ya amince a rantsar da shi a gaban kotun kolin kasar, to amma tuni ya yi jawabin rantsuwar kama aiki a gaban dubban magoya bayan sa a dandalin Tahrir a jiya Jumua.

Karin bayani