Shugaba Mursi ya karbi ragama a hukumance

Shugaba Muhammad Mursi na Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Muhammad Mursi na Masar ya karbi ragama a hukumance

Shugaban kasar Masar farar hula kuma mai kishin Musulunci na farko, Muhammad Mursi, ya sha rantsuwar kama aiki tare da yin kira da a maido da majalisar dokokin da aka rushe kwanan baya.

Yayin wani biki a wani barikin soji da ke wajen birnin Alkahira, shugaban Majalisar Mulkin Sojin kasar, Field Marshal Mohammed Tantawi, ya mika ragamar mulki a hukumance ga Shugaba Mursi.

Kafin nan dai a jawabinsa na farko a Jami'ar Alkahira, ya ce zai kare rundunar sojin kasar a matsayinta na cibiyar kasa; amma kuma ya yi gargadin cewa sojojin ba za su taba zama makwafin muradun al'ummar kasar ba.

“Majalisar kolin soji ta cika alkawarin da daukarwa kanta cewa ba za ta zama makwafin muradun al'umma ba”, in ji Mista Mursi, wanda ya kara da cewa, “Zababbun cibiyoyi za su dawo don gudanar da ayyukansu, su kuma sojoji za su koma nasu aikin na tsaron kasa”.