Masu kishin Islama sun rusa kushewar Wali, Sidi Mahmoud

Masallaci da cibiyar karatu a Tikbuktu Hakkin mallakar hoto none
Image caption Masallaci da cibiyar karatu a Tikbuktu

Mazauna garin Timbuktu na kasar Mali, wanda daya ne daga cikin wurare masu tarihi na majalisar dinkin duniya sun ce mayakan sa kai masu zafin kishin Islama sun rushe kushewar wani shaharren waliyyi na karni na 15, Sidi Mahmoud.

Sun kuma ce ana kai hari a kan kushewar wasu waliyyan.

Wani mai magana da yawun kungiyar masu zafin kishin Islama ta Ansaruddeen wacce ke iko da galibin arewacin kasar ta Mali ya ce za a rushe duk wata kushewa da ke garin.

Hukumar kula da al'adu ta majalisar dinkin duniya , UNESCO, ta ce rushe-rushen abin takaici ne, ta kum ayi kira ga kungiyar ta Ansaruddin ta dakatar da su.

Hukumomi a Bamako, babban birnin kasar sun kwatanta al'amarin da aikata laifukan yaki.

Kungiyar ta Ansaruddeen ta yi amanna cewa bautawa waliyyai haramun ne a Musulunci.

A farkon shekarar nan 'yan gwagwarmaya na masu kishin Islama da kuma yan tawayen Azbinawa suka kwace iko da arewacin Mali sakamakon wani juyin mulki.

Karin bayani