An rantsar da sabon Shugaban Masar, Mohammed Morsi

Mohammed Morsi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mohammed Morsi

Shugaban kasar Masar farar hula kuma mai kishin Musulunci na na farko, Muhammad Mursi, ya sha rantsuwar kama aiki tare da yin kira da a maido da majalisar dokokin da aka rushe kwanan nan.

A jawabinsa na farko a Jami'ar Alkahira, ya ce zai kare rundunar sojin kasar a matsayinta na cibiyar kasa; sai dai kuma ya yi gargadin cewa sojojin ba z asu taba zama makwafin muradun al'ummar kasar ba.

Ya kuma yi alkawarin bude wani sabon babi a tarihin kasar:

Yayin da yake jawabin nasa, iyayen wadanda aka kashe a karkashin mulkin Hosni Mubarak sun yi ta daga hotunan 'ya'yan nasu.

To sai dai babban kalubale gare shi, shi ne daidaita harkokin mulki alhali yawancin iko na hannun dakarun sojin kasar.

Karin bayani