Bam ya tashi a kan gada a Jihar Filato

Wani harin bam a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani harin bam a Najeriya

Wani bam ya fashe a kan wata gada a karamar Hukumar Riyom ta jihar Filato ta Najeriya, inda aka dasa bama-bamai a saman gadar da kuma karkashinta.

Hukumomin tsaro dai sun bayyana cewa bama-bamai biyu ne aka dasa, inda daya ya tashi jiya da tsakar dare yayin da jami'an tsaron suka kwance dayan da bai tashi ba.

Kodayake dai an sha samun tashe-tashen bama-bamai a jihar ta Filato da ma wasu jihohi na Nijeriya, wannan shi ne karon farko da aka samu tashin bama-bamai a yankin karkara a jihar.