An kama jagoran masu fasa bututan mai a Najeriya

Yan gwagwarmayar Naje Delta Hakkin mallakar hoto b
Image caption Yan gwagwarmayar Naje Delta

Sojoji a Najeriya sun ce sun cafke mutumin da ake zargin shi ne ke jagorantar gungun barayin da ke kai hare hare a kan bututun mai a yankin Naija delta.

Ana zargin Seifa Gbereke, wanda kuma ake yiwa lakabi da Janar Cairo da satar danyen mai daga bututan mai, lamarin da ke janyo wa Kasar data fi kowacce samar da danyen man a nahiyar afirka asarar dala biliyan biyar a duk shekara, kamar yadda kiyasi ya nuna.

Wannan dai wata nasara ce babba, idan aka yi la'akari da cewar ya jima yana addabar yankin Neja Delta baki daya, inji Kanar Oyeama Nwachukwu, kakakin rundunar hadin guiwar tsaro a yankin.

Gbereke, wanda aka ce shekarunsa 25, ana zarginsa da yin makarkashiyar kai hare haren bama bamai a kan bututan mai da rijiyoyin man a Jihohi 3 na kasar dake da mafi yawan arzikin mai , wato jihohin Bayelsa da Delta da kuma Rivers.

Satar mai dai wata matsala ce dake ta karuwa a Najeriya,kuma Shugaban kamfanin mai na Shell, Peter Voser ya ce a cikin watan Afrilu an yi kiyasin cewar ana satar gangar mai kimanin dubu dari da hamsin a kasar a kowace rana.