Kofi Annan ya gargadi kasashen duniya kan rikicin Syria

Kofi Annan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kofi Annan da sauran masu taro a Geneva

Wakilin majalisar dinkin duniya mai yunkurin samar da zaman lafiya, Kofi Annan, ya gargadi ministocin harkokin wajen kasashen da ke taro a kan Syria cewa idan suka kasa cimma matsaya a kan yadda za a shawo kan rikicin da ake fama da shi, to tashe-tashen hankulan ka iya yaduwa zuwa matakin kasa-da-kasa.

Mista Annan ya shaidawa taron ministocin a Geneva cewa alhakin karuwar mutuwar al'ummar Syria zai rataya a wuyansu idan suka kasa kulla wata yarjejeniya.

Ministan harkokin wajen Burtaniya, William Hague, ya ce wajibi ne kasashen duniya su cimma matsaya ba tare da bata lokaci ba:

Ya ce ina ganin yana da matukar muhimmanci a tunkari wannan tataunawa ta yau da tunanin cewa akwai bukatar daukar matakan da suka dace da gaggawa, domin yanayi a Syria kara tabarbarewa yake yi.