Za a bude taro a Geneva da nufin kawo karshen rikicn Syria

Sergie Lavrov da Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sergie Lavrov da Hillary Clinton

Yau za a fara wani taro a Geneva wanda zai duba hanyoyin da za a magance rikicin da ake yi a kasar Syria.

Alamu na nuna cewar akwai rashin jituwa tsakanin Rasha da kasashen Yammacin duniya dangane da ko za a kyale Shugaba Assad ya cigaba da mulkin kasar.

Rasha wadda aminiya ce ga Mr Assad ta na cigaba da nuna rashin amincewa da bukatun cewar lallai a tumbuke shi daga mulki.

Yunkurin diflomasiyyar dai, da wuya ya yi aiki ba tare da hadin kan kasar Russia ba.

Kodayake, a wata ganawa da suka yi kafin taron da sakatariyar kula da harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ministan kula da harkokin wajen Russia Sergie Lavrov ya nuna cewa za a iya cimma maslaha game da batun na Syria.

Karin bayani