An kashe mutane fiye da ashirin a Congo

Wani sojan gwamnatin Congo yana gadi a wani sansanin soji Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani sojan gwamnatin Congo yana gadi a wani sansanin soji

An kashe mutane fiye da ashirin lokacin da 'yan tawaye suka kai hari a kan wani sansanin soji da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

Wadansu sojojin da suka gudu daga wuraren aikinsu da 'yan tawayen Mai Mai ne dai suka kaddamar da harin a yankin Lubero ta Kudu.

Kungiyoyin agaji sun ce rashin bin doka ya karu a yankin saboda hankalin dakarun kasar ta Congo ya yi wani wurin, inda suke yakar wadansu 'yan tawayen da ake kira M23, wadanda kwararrau daga Majalisar Dinkin Duniya suka ce Rwanda na goyawa baya.

Sakamakon haka babu wani tsaro na a zo a gani a wadansu sassan yankin mai kungurmin dazuzzuka, kuma dubban daruruwan mutane sun tsere daga gidajensu don gujewa hare-haren kungiyoyin 'yan tawaye iri-iri.