Kungiyar Turai ta haramta wa wakilanta sayen man Iran

Matatar man Iran
Image caption Matatar man Iran

A yau ne wani takunkumin hana shigar da man fetur na Iran cikin kasashen Tarayyar Turai yake fara aiki.

Wannan mataki dai wani bangare ne na yunkurin da Tarayyar ta Turai da Amurka ke yi na kara matsin lamba a Tehran da dakatar da shirnta na nukiliya.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya bayyana sa a matsayin mataki mafi tsauri kawo yanzu da kungiyar taarayyar turai ta dauka kan Iran.

Takunkumin dai ba harkar fitar da man fetur kawai ya shafa ba; ya hada har da samar da kudade da inshorar jigilar man.

Hanin sayen man da kungiyar ta EU ya zo ne daf da lokacin da matakan Amurka dake yin barazana saka takunkumi a kan duk wata kasa da ta yi amannar cewar ba ta yi wani hobbasa na rage danyen man da take saye daga Iran ba,ke fara aiki.

Wannan ya shafi manyan abokan cinikayyar Iran a Asiya.

China da Japan da India da kuma Koriya ta Kudu duk sun rage yawan man da suke saye daga Iran, inda Koriya ta Kudu ke shirin dakatar da saye baki daya.

A sakamakon wannan mataki na kungiyar EU da Amurka, za a iya kiyasta cewar man da Iran ke fitarwa zai ragu da kusan ganga miliyan daya a rana.

A zahiri wannan na nufin asarar dola kusan biliyan 8 na kudin shiga a kowanne watanni 3.

Mr Hague ya ce manufar takunkumin shi ne na shawo kan Iran ta sasanta da gaske game da shirinta na Nukiliya.

Karin bayani