Yanbindiga sun kai a Unguwar Kurna ta Kano

Taswirar Najeriya mai nuna gurbin Kano
Image caption Taswirar Najeriya mai nuna gurbin Kano

Wasu mutane uku sun rasa rayukansu a Unguwar Kurna dake cikin birnin Kano a arewacin Najeriya a lokacin da wasu yan bindiga suka bude wuta ba tare da rarrabewa ba.

Mazauna Unguwar sunce, 'yan bindigar sun shiga unguwar sun fara harbi ne tun daga farkon layin inda suka harbe wani tsohon kansila har lahira suka kuma jefa wani abu mai fashewa a cikin gidansa.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka kai hari makamancin wannan a yankin na Kurna tun lokacin da aka fara kai hare-hare a birnin na Kano cikin watan Janairun bana.

Rundunar yansanda ta jihar dai ta tabbatar da kai harin , amma ta bayyana cewar maharan sun arce kafin isar jami'anta a wurin.

Babu dai wanda ya dauki alhakin kai harin , sai dai kungiyar Ahlissunna liddaawati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram na amsa alhakin kai hare hare a yan watannin nan a birnin.