An kai hari a kan majami'u biyu a Kenya

Jami'an tsaro na fitar da gawar wata mata bayan harin na Garissa Hakkin mallakar hoto Associated Press
Image caption Jami'an tsaro na fitar da gawar wata mata bayan harin na Garissa

Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a Kenya ta ce mutane goma sha shida sun rasa rayukansu lokacin da aka kai hari a kan wadansu majami'u biyu.

Babban Jami’in KIwon Lafiya na Lardin Arewa maso Gabas, Mahamad Abey Shekh, ya ce mutane goma sha biyar ne suka rasa rayukansu, yayinda arba’in da bakwai suka jikkata—bakwai daga cikinsu kuma suna can rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

An yi harbe-harbe ne, sannan aka jefa gurneti a kan majami'un da ke Garissa a arewa maso gabashin Nairobi, babban birnin kasar, a kan hanyar zuwa iyakar kasar da Somalia.

Wadansu 'yan sanda biyu masu gadin majami'un suna cikin mutanen da suka rasa rayukansu.

Wani ganau ya shaidawa BBC cewa ba a ganin kowa a kan titunan garin sai jami'an tsaro:

“Garin cike yake da 'yan sanda. Duk mutane sun shige gida, ba wanda ke fitowa.

“Lokacin da al'amarin ya faru 'yan sanda sun yi ta kama duk wanda suka gani a garin, da ma kusa da wurin, shi ya sa mutane suka yiwa kansu kiyamullaili.

Tun bayan da Kenya ta kutsa cikin Somalia don yakar mayakan al-Shabaab ne dai ake ta kai hare-hare a cikin kasar.

Karin bayani