Mutane 15 sun mutu a harin da aka kai Kenya

Jami'an tsaro na fitar da gawar wata mata a daya daga cikin majami'un da aka kaiwa hari a Kenya Hakkin mallakar hoto Associated Press
Image caption Jami'an tsaro na fitar da gawar wata mata a daya daga cikin majami'un da aka kaiwa hari a Kenya

Jami'an kasar Kenya sun ce akalla mutane 15 ne aka hakikance sun rasa rayukansu a hare-haren da aka kai kan wasu majami'u biyu a gabashin garin Garissa.

A majami'a ta farko dai gurneti aka jefa yayin da 'yan bindiga suka kutsa cikin majami’a ta biyu suka yi ruwan harsasai.

Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross na kwashe wadansu daga cikin mutanen da suka yi munan raunuka ta jiragen sama.

Wani jami'in gwamnati ya ce jami'an tsaro da dama na farautar maharan, amma kuma gidan talabijin na Kenya ya bayar da rahoton cewa sun tsere.

A cewar gidan talabijin din, “Nan take maharani—wadanda aka raunata daya daga cikinsu—suka tsere.

“An kuma bayar da rahoton cewa sun yi awon gaba da bindigohgi biyu na 'yan sanda”.

Garin na Garissa dai a arewa maso gabashin Nairobi, babban birnin kasar, yake a kan hayar zuwa iyakar kasar da Somalia.

Wadansu 'yan sanda biyu da ke gadin majami'un suna cikin mutanen da suka rasa rayukansu.

Wani ganau ya shaidawa BBC cewa ba a ganin kowa a kan titunan garin sai jami'an tsaro.

“Garin cike yake da 'yan sanda; duk mutane sun shige gida ba wanda ke fitowa.

“Lokacin da al'amarin ya faru 'yan sanda sun kakkama duk wanda suka samu a garin, da ma wadanda ke kusa da wurin, shi ya sa mutane suka yiwa kansu kiyamullaili”.

Tun bayan da Kenya ta kutsa cikin Somalia don yakar mayakan al'Shabaab ne dai ake ta kai hare-hare a cikin kasar.

Karin bayani