An bude runfunan zaben yan majalisar dokokin Senegal

Zaben yan majalisa a Senegal Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zaben yan majalisa a Senegal

Alummar kasar Senegal dake yammacin Afirka sun je rumfunan zabe a yau don kada kuri'unsu a zaben yan majalisun dokokin kasar guda 150.

Zaben zai zamanto wani zakaran gwajin dafi ga farin jinin sabon shugaban kasar Macky Sall bayan nasarar da ya samu a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka yi a watan Maris da ya gabata.

Dukkanin shugabannin siyasar kasar da suka goyibayan Macky Sall bisa adawarsu da tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade, wanda ya nemi cigaba da mulki a waadi na ukku bayan cikar waadinsa a farkon wannan shekara, har yanzu su na tare, da nufin tabbatar da samun kaso mai yawa a majalisar dokokin kasar.

Wannan zaben, shi ne karon farko da mata za su samu damar yin zabe daidai da maza a tsarin dokar kasar.

Gamayyar jamiyyun adawar dai na da babban kalubale na shawo kan matsalolin da alummar kasar ke fama da shi kamar fari da tashin farashin kayan masarufi.

Karin bayani