Turkiya ta tura jiragenn yakinta zuwa kan iyaka da Syria

Jirgin yakin Turkiya
Image caption Jirgin yakin Turkiya

Rundunar sojin Turkiyya ta ce ta aike da jiragen saman yakinta guda shidda kan iyakar kasar da Syria, bayan wasu jiragen Syria masu saukar ungulu sun yi shawagi a kusa da kan iyakar.

A cikin wata sanarwa sojin sunce -- daga karshe -- dai ba a keta sararin samaniyar Turkiyar ba.

Ruguguwar tayar da jiragen yakin dai wata alama ce ta ci gaba da zaman dar dar din dake tsakanin Turkiya da Syria.

Syria ta ce jirgin saman na tafiya ne a sararin samaniyar Syria -- wani zargin da Turkiya ta musanta.

A watan jiya ne dai Syria ta kakkabo wani jirgin yakin Turkiyya, kuma tuni Ankara ta yi gargadin cewa duk wani ayarin sojin Syria da ya kusanci iyakarta za ta dauke shi a matsayin barazana.

A halin da ake ciki kuma, majalisar 'yan adawa ta Syria, wato Syria National Council, ta yi watsi da duk wani shiri da zai kyale Shugaba Assad ya ci gaba da mulki:

Mai magana da yawun majalisar ke nan Khalid Saleh yake cewa maslaha muke nema ta siyasa wadda za ta magance rikicin Syria ta kawo karsehn zub da jini. Don haka ba za mu yarda Assad da wadanda hannayensu suka yi dumudumu da jinin al'umma su ci gaba da mulki ba.

Karin bayani