Shugaban bankin Barclays ya yi murabus

Marcus Agius Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Shugaban hukumar daraktocin bankin Barclays Marcus Agius

Shugaban hukumar daraktocin daya daga cikin bankunan da suka fi girma a duniya, wato Barclays, ya yi murabus bayan ta tabbata cewa wadansu ma'aikatan bankin sun yi coge wajen tsayar da kudin ruwan da bankuna kan karba ko suke biya.

Wanda ya yi murabus din, Marcus Agius, ya ce ya dauki alhakin abin da ya kira wani gagarumin koma-baya ga kimar bankin.

Daya daga cikin masu jari a bankin, Max King, ya ce “A irin wannan lokaci da bankin Barclays ke fuskantar manyan kalubale, murabus din shugaban bankin ma wani babban koma-baya ne”.

Sai dai kuma Babban Jami'in da ke kula da gudanar da bankin, Bob Diamond, ya ci gaba da kasancewa a kan mukaminsa.