An lalata shelkwatar hukumar zabe a Benghazi

Masu zanga zanga a Benghazi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Benghazi

Masu zanga zanga a birnin Benghazi na kasar Libya da sauran yankuna a gabashin kasar sun aukawa ofishin hukumar zaben kasar a cikin dare.

Bukatarsu ita ce a sake nazari kan kujerunda aka ware wa yankunan kasar a zaben da ke tafe na yan majalisar dokoki.

A ranar asabar ce mai zuwa yan kasar ta Libya za su je runfunan zabe a karon farko cikin kusan rabin karni, don zaben yan majalisun dokoki.

Masu zanga zangar a birnin Benghazi sun aukawa ofishin hukumar zaben kasar inda suka lalata akwatunan zabe da komputoci da takardun bayanan da suka gani a cikin ofishin.