'Yan Ansarudeen sun kammala rushe hubbaren waliyai a Mali

timbuktu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Ansaruddeen sun kammalla rushe hubbare a Mali

Masu kaifin kishin Islama a arewacin Mali sun kammala rushe hubbaren wasu waliyai dake birnin Timbuktu duk da nuna adawa da yin hakan da wasu suka nuna.

Su dai 'yan kungiyar ta Ansar-Deen da suka dau makamai sun ce, alamomi da suka kamar hubbaren waliyai da suka zarta shekaru dari sun sabawa musulunci, suna masu cewa, bai kamata a samu wani shamaki ba tsakanin mutane da mahallicinsu.

Babbar mai shigar da kara ta Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya, Fatou Bensouda, ta kwatanta al'amarin da aikata laifuffukan yaki, sannan ta yi barazanar gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a gaban kotun ta duniya.

A wata hira da ta yi da Sashen Faransanci na BBC, Ministar Al'adu ta kasar ta Mali, Fadima Toure Diallo, ta yi Allah-wadai da rushe-rushen.

“Suna nan suna kai hare-hare a kan hubbaren waliyyai da dama da kuma dukannin wuraren tarihi na wannan gari, wanda birni ne da Majalisar Dinkin Duniya ta hannun [hukumarta mai kula da al’adu,] UNESCO, ta baiwa matsayi na musamman a [jerin wurare masu daddaden tarihi.

“Abin da ke faruwa yana da ban takaici: Tumbuktu, gari ne da ya yi fice, kuma akwai waliyai dari uku da talatin da ke da hubbaren su a can”.

Minista Fadima Toure ta kuma bayyana masu fafitikar na kungiyar Ansarud Deen da cewa 'yan ta'adda ne:

“’Yan ta'adda ne; mutane ne wadanda ba su da imani ko kadan, kuma ba sa bin doka.

“Suna fakewa da sunan wani addini domin su lalata wurare masu muhimmanci, amma mu a nan Mali ba mu san irin wannan salon addinin da suke bi ba ko kadan”.

Karin bayani