Za a gina sabbin matatun man fetur shida a Najeriya

mai Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Matatar danyen man fetur

Gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu akan wata yajejeniya da wani kamfanin Amurka mai suna Vulcan Energy na gina wasu matatun mai guda shidda a kasar.

Ana sa ran sabbin matatun man da za a gina kan kudi kimanin dala miliyan dubu hudu da dari biyar, zasu rika sarrafa danyen mai da ya kai ganga dubu dari da tamanin a kowace rana.

Wata sanarwa data fito daga hannun kakakin ma'aikatar ciniki ta Najeriya Yemi Kolapo, ta ce ana saran kammala gina biyu daga cikin sabbin matatun man guda shida ne nan da shekara mai zuwa, yayin da sauran ake saran kammala su bayan watanni 30.

A cewar kakakin ma'aikatar ciniki ta Najeriyar, gwamnatin kasar na saran idan aka kammala ginin matatun man, kowace matatar mai za ta rika sarrafa danyen mai kimanin ganga dubu 30 a kowace rana, tare kuma da samar da litar miliyan biyar na man fetur da man diesel da kuma kalanzir.

A wata hira da kamfanin dillacin labaru na Reuters, Chief Edozie Njoku, wanda shine jagoran kamfanin na Amurka wato Vulcan Energy, a Najeriya ya ce burin kafa matatun man shine a rarraba su a kowace shiya ta kasar ta yadda kowace shiyya dake kasar zata samu matatar mai guda.

Wannan yarjejeniyar gina sabbin matatun mai da gwamnatin Najeriyar ta kulla na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu masu lura da al'amura Najeriyar ke ganin kasar bata bukatar gina wasu sabbin matatun mai kasancewar har yanzu matatun mai guda hudu da take dasu sun kasa tsayawa da kafafunsu.

Karin bayani