'Ana samun yawaitar makamai a Syria'

Hakkin mallakar hoto s
Image caption Navi Pillay

Babbar Jami'a mai kula da kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay, ta yi gargadin cewa bai wa gwamnati da 'yan adawa a Syria makamai shi ne ke kara rura wutar rikicin da aka dauki watanni 16 ana yi.

Misis Pillay tana magana ne bayan yi wa Kwamitin Tsaro na Majalisar bayani game da halin ake cikin a kasar ta Syria ta fuskar kare hakkin dan adam.

Babbar Jami'ar dai ba ta bayyana wuraren da makaman ke fitowa ba duk da cewar Rasha ita ce babbar mai samarwa gwamnati da makamai yayin da Saudiyya da kuma Qatar ke tallafawa 'yan tawaye da makaman kuma suke biyansu albashi.

Misis Pilay ta bayyana cewa a yanzu sunan yakin da ake yi a syria 'fadan cikin gida', wanda ta ce ya wajaba dukkanin bangarorin da ke fada da juna a ciki su zama wadanda za a iya hukunta wa a karkashin dokar kasa-da-kasa.

'Keta hakkin bil adama'

A cewar Misis Pilay duk sojan gwamnati dana 'yan tawaye sun aikata cin zarafin bil adama kuma tayi imani cewar akwai hujjojin da ke nuna hakan.

Ta nanata kiran da take yi wa Kwamitin Tsaron na ya mika batun Syria ga Kotun Hukunta Manyan Laifukka ta Duniya.

Kwamitin dai na duba yiwuwar rage yawan tawagar masu sanya idon da Majalisar Dinkin Duniyar ta tura zuwa Syria tun da fada ya sanya ba ta iya yin wani aiki a can.

Amma Misis Pillay ta bukaci a kara wa tawagar iko ta yadda za ta iya bayar da bayanai a kan ayyukan keta hakkin dan adam da ake yi a Syria yadda ya kamata.

Kodayake dai masu sanya idon sun daina duba abubuwanda ke wakana a askasarin sassan kasar amma suna cigaba da ziyartar asibitoci.

Misis Pillay ta ce dakarun gwamnati na kai hari asibitoci yayin da su kuma 'yan tawaye suka kwace iko da wani asibiti domin ayyukan soji.

Karin bayani