Diamond ya amsa tambayoyi gaban kwamitin majalisa

diamond Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tsohon shugaban bankin Barclays, Bob Diamond

Tsohon shugaban gudanarwa na bankin Barclays a Birtaniya wanda yana cikin manyan bankuna a duniya, ya fuskantar tambayoyi a bainar jama'a dangane da badakalar da ta shafi bankin wacce kuma ta raba shi da mukaminsa.

Kwana guda bayan yayi murabus, Bob Diamond ya bayyana a gaban kwamitin baitul-mali na majalisar dokokin Birtaniya.

Akwai yiwuwar zai fuskanci tambayoyi akan cogen da ya shafi kudin ruwa:

Wakilin BBC yace "tuni manyan 'yan siyasa suka ce, murabus din Mista Diamond zai bada wata damar kawo gyara a harkar banki a Birtaniya dake fama da matsaloli".

Karin bayani