Kotun Duniya ta bukaci bincike a kan 'Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Babbar mai shigarda kara a kotun duniya Fatou Bensouda

Sabuwar shugabar kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Fatou Bensouda, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta gudanar da bincike a kan hare-haren da 'yan Kungiyar Jama'atu Ahlissunnah Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram suka yi ikirarin kai wa a kasar.

Babbar mai gabatar da karar ta yi wannan kiran ne lokacin da ta kai ziyara Najeriya inda ta ce kawo yanzu kotun ba ta gudanar da wani bincike a hukumance ba a kan rikice-rikicen da ake fama da su a arewacin Najeriyar, amma ta yi wani kwarya-kwaryan nazari a kan ayyukan kungiyar.

Fatou Bensouda ta shaidawa manema labarai cewa ana aikata miyagun laifuka a kasar wadanda za a iya kira hare-haren ta'addanci; kuma za a iya saka su cikin jerin ayyukan cin zarafin bil adama.

Sai dai ta jaddada cewa kotun ba za ta shiga cikin batun ba muddin Najeriya ta dauki matakan shari'a wajen shawo kan lamarin.

Hasalima ta ce hakkin gwamnatin Najeriyar ne ta gudanar da cikakken bincike.

Shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan dai ya tabbatar wa babbar mai shigar da karar cewa gwamnati ba za ta kawar da kai ba ta bari ana aikata manyan laifukka ba tare da daukar mataki ba.

Fatou Bensouda dai ita ce 'yar Afrika ta farko da ta hau kan wannan kujerar ta babban mai shigar da kara ta kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ke birnin Hague inda ta maye gurbin Louis Moreno Ocampo.