Burtaniya za ta rage yawan sojojin ta

Hakkin mallakar hoto PA

Gwamnatin Burtaniya za ta zabce manyan rundunoni soji goma sha bakwai a kasar, wadanda suka hada harda bataliyoyi biyar na sojin kasa, don rage yawan kudin da gwamnati ke kashewa.

Za a rage yawan sojojin yau-da-kullum don ya koma zuwa kimanin dubu tamanin, wanda shine yawa mafi kankanta a cikin shekaru dari biyu da suka gabata.

Gwamnatin ta ce nan gaba illahirin rundunar sojin Burtaniyar za ta kasance kashi biyu ne -- kashin karfo shi ne na rudunonin kai-dauki da suka hada da sojojin yau-da-kullum da kuma dakarun ko-ta-kwana wadanda suka hada da sojojin wucin-gadi.

Jam'iyyar adawa ta Labour ta ce shirin rage rundunonin sojin wani gurgun mataki ne na tinkarar barazana kuma da tashin hankalin da ake fuskanta a duniya.

Karin bayani