An kafa kwamitin nazari kan batun rarar kudin mai

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Gwamnatin Najeriya ta sake kafa wani kwamitin da zai daidaita sakamakon binciken da ma'aikatar kudin kasar ta gudanar a kan yadda aka gudanar da biyan kamfanonin man da suka yi harkar ba da tallafin mai a kasar.

Gwamnatin ta ce ta kafa kwamitin ne da nufin cika alakawarin da shugaban kasar ya yi cewa gwamnatinsa ba za ta sassauta wajen hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin cuwa-cuwar da ake zargi wasu kamfanonin sun yi a shirin ba da tallafin ba.

Karin bayani