Kotu ta samu tsoffin Shugabannin Argentina da satar Jarirai

videla and bignone Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsoffin shugabannin mulkin sojin Argentina da kotu ta samu da laifi.

Wata kotu a Argentina ta samu tsofaffin shugabannin sojin kasar biyu da laifin jagorantar sace jariran da fursunonin siyasa suka haifa.

Kotun wadda ke a Birnin Buenos Aires ta yankewa Jorge videla hukumcin daurin shekaru 50 da kuma Reynaldo Bignone hukumcin daurin shekaru 15.

Akalla jarirai dari hudu ne ake jin an sace a lokacinda sojojin suka yi mulki tsakanin shekarun 1976 da kuma 1983.

Mai shara'a Maria Roqueta ce ta karanta hukumcin a gaban zauren kotun wanda ke cike makil da mutane; inda tace an yankewa Jorge Videla da hukumcin dauri shekaru 50 saboda kasancewar sa babban mai laifi wajen sacewa, da kuma boye kananan yaran.

Yadda wadanda lamarin ya shafa suka ji

Wasu daga cikin iyayen jariran da aka sace da ke raye har yanzu, da danginsu da masu rajin kare hakkin dan adam da suka da suka taru a wajen kotun dai sun yi maraba da hukumcin da aka yanke wa tsoffin shugabanin biyu ta hanya fashewa da sowa da kuma tafi.

Estela de Carlotta shugabar wata kungiyar kare hakkin dan adam ta Grandmothers of the Plaza de Mayo, wadda aka kafa domin gano jariran da aka sace lokacin mulkin sojin a Arjentina cewar takeyi: '' wannan shine adilci. Ga shi nan yazo.Ina tuna cewar mun fara wannan fafutikar ce tun a 1996, kuma a lokacin bamu da masaniyar ko zamu iya kawowa wannan matakin kuma mu ga hakan da ranmu.Ina jin abune mai faranta zuciya ga al'umma ta ji an yi musu hukumci kuma an yin tir da su.''

Sai dai a yayinda wasu da wadanda abin ya shafa ke murna da hukumcin, wasunsu na ganin har yanzu da saura, domin akwai sauran wadanda suma ya kamata a hukumta su.

''Muna da wani babban aiki da ba a yi ba saboda har yanzu ba a hukumta mutanenda ba sojiji ba dake da hannun a ciki ba. Indai mun ce anyi kisan kiyashi, to dole ne a hukumta wadannan mutanen.'' Inji Maria Victoria Moyano daya daga cikin wasu jarirai 34 da aka sace wadanda suna daga cikin masu shigarda kara a shara'ar.

Dama duka mutanen biyu dai na daure ne a gidan yari bayanda a can baya wata kotu ta same su da laifi cikin aiyukan keta hakkin dan adam da aka tafka lokacin mulkinsu.

Karin bayani