'Yan tawaye sun kwace Bunagana a Congo

'Yan tawaye a gabacin Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo sun kwace garin Bunagana dake kan iyaka da Uganda.

Mai magana da yawun kungiyar 'yan tawayen ta M23 ya ce ta na da cikakken iko da yankin bayan wani kazamin fadan da suka gwabza da sojojin gwamnatin Congon.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe mata daya daga cikin sojojinta 'yan kasar India dake aikin kiyaye zaman lafiya a artabun.

Jami'an Uganda sun ce sojojin Congo kusan 600 ne suka tsere zuwa Uganda, tare kuma da dubban yan gudun hijira.

Bata-kashi

Wani sojan gwamnatin Uganda, Kanal Peter Elwelu, ya ce: "An shafe watanni ana bata-kashi, amma sai ajiya ne suka karasa kan iyaka kuma suka kwace (garin). Amma sai da aka yi ta arbatu na kusan sa'oi 24 kafin su iya kwace yankin".

Akan fargabar cewar za a iya ganin Uganda kamar tana tsoma baki a cikin al'amurran Congo, Kanar Elwelu yace sam ba haka abin yake ba.

Yace: "Ba na tunanin haka. Ina ganin cewar 'yan Congo za su magance matsalarsu a matsayinsu na 'yan Congo".

Ita dai Majalisar Dinkin Duniya ta na zargin kasar Rwanda ne da nuna goyon bayanta ga 'yan tawayen M23 na Congo wadanda suka dade suna fafatawa da dakarun gwamnatin Jamhuriyar Congon.

Karin bayani