Libya na shirin yin zabe

zabe a Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption yan takara na neman kuriu

Libya na shirin yin zabe a karon farko tun bayan hambarar da mulkin Colonel Gaddafi da kuma kashe shi.

zaben dai za ayi ne wanda zai samar da sabuwar majalisa wadda za ta za bi gwamnatin da zata mika mulki ga farar hula.

Zaben dai za a yi shi cikin matsalolin tsaro da kuma rarrabuwar kawuna tsakanin gabashi da Yammacin kasar

Watanni tara bayan hambarar da gwamantin Colonel Gaddafi yanayin siysar kasar na cikin rashin tabbas.

Zaben yan majalisun dai zai samarda majasalisa mai mambobi dari biyu.

Amma rawar da zata taka shine ta mika mulki; inda za ta za bi Prime Minista da kuma mukarrabai wadanda zasuyi zaben gama gari a karkashin sabon kundin tsarin mulki shekara mai zuwa.

Karin bayani