Kasashen duniya za su taimakawa Afghanistan da dala biliyon 16

afghanistan
Image caption Taron akan Afghanistan a Tokyo

Kasashe masu bada agaji dake taro a Tokyo sun yi alkawarin bada gudunmawar biliyoyin daloli domin taimakawa Afghanistan.

Sai dai kuma kasashen sun bukaci gwamnatin kasar da ta dauki matakan yaki da cin hanci da rashawa.

Mahalarta taro daga kasashe sama da saba'in sun yi alkawarin bada dala biliyan goma sha shidda, domin taimakawa Afghanistan, har zuwa lokacin da za a janye dakarun da NATO ke jagoranta a 2014 da kuma bayan hakan.

Ministan harkokin wajen Afghanistan, Zalmai Rassoul kenan, ya ce "gwamnatin Afghanistan ta yi alkawarin ci gaba karfafa jaririyar dimokradiyyarmu, da kyautata shugabanci da kuma yaki da cin hanci da rashawa".

Karin bayani