'Yan sanda sun kama shugabannin dalibai a Burma

police Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda a kasar Burma

'Yan fafutukar kafa dimokradiyya a Burma sun ce an kama shugabannin dalibai su sama da ashirin a duk fadin kasar, a wani samame mafi girma na kama masu adawa, tun bayan da aka bullo da sauye sauyen siyasa a kasar bara.

Wakilin BBC ya ce an kama biyar daga cikin su ne a Rangoon, inda Kyo Kyo Gyi, wani tsohon jagoran dalibai a boren 1988 ke cewa, hukumomi cewa suka yi zasu yi wata ganawa da su.

An tsare su ne gabanin fara bukukuwan cika shekaru hamsin na zagayowar ranar murkushe wani boren dalibai.

Mutane kimanin dari uku ne suka hallara a Rangoon domin halartar gangamin, duk da kamen da aka yi da kuma baza 'yan sanda cikin farin kaya.

Karin bayani