An kashe mutane 37 a tashin hankali a kauyukan Jos

jos
Image caption Tashin hankali a Jos

Rundunar soja a Najeriya ta ce an kashe mutane talatin da bakwai,bayan wasu hare haren da aka kai kan wasu kauyukan Kiristoci,kusa da birnin Jos.

Wani mai magana da yawun sojan Kaptin Mustapha Salisu ya ce jami'an tsaro sun shafe sa'o'i suna artabu da wadanda ya kira kwararrun mahara.

Ya ce an kashe ashirin daga cikin maharan.

Wani mai magana da yawun wata kungiyar Kiristoci ya ce an kai hare hare a kan kauyuka goma sha uku.

A 'yan shekarunan dai ana yawaita samun tashin hankali na kabilanci, da kuma na addini tsakanin Musulmi da Kirista a Jos da kewaye.

Karin bayani