An kashe mutum daya a ranar zabe a Libya

libya
Image caption Masu zabe a Libya

Al'ummar kasar Libya na kada kuri'a a zaben farko na kasa cikin kusan shekaru hamsin.

'Yan takara fiye da dubu uku ne suke takarar majalisar dokokin kasar wadda zata maye gurbin majalisar rikon kwaryar kasar da aka kafa bayan kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi watanni tara da suka wuce.

Rahotanni na cewa an kashe mutum guda a lokacin wata musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zanga a garin Ajdabiya, an kuma raunata wasu biyu.

Ana gudanar da zaben ne a cikin zaman dar dar, a yayinda aka dakatar da zabe a garuruwan Ajdabiya da Brega dake gabashin kasar ta Libya, saboda zargin sace takardun zabe da hatimi.

Kamila Rafifi na daya daga cikin wadanda suka kada kuri'a a birnin Tripoli.

Ta shaidawa BBC cewar "Ji nake kamar wani babban mafarki. Ban taba tsammanin zan ga wannan rana ba a rayuwata, wannan abu ne na tarihi".

Karin bayani