'Yan bindiga sun kashe Sanata Gyang Dantong a Barkin Ladi

Gyang Dantong Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sanata Gyang Dantong

Rahotanni daga jihar Filato a Najeriya na cewa wasu manyan 'yan siyasa sun rasa rayukansu a wani sabon tashin hankali da aka yi dazu a yankin Barkin Ladi.

Bayanai dai na cewa Sanata Gyang Dantong dake wakiltar mazabaar arewacin jihar Filato a majalissar dattawan Najeriya da kuma Mista Gyang Fulani, sun rasa rayukansu ne a yayin da wasu 'yan bindiga suka bude masu wuta.

'Yan siyasar dai na cikin dimbin mutane ne 'yan kabilar Berom dake halartar jana'izar mutane da dama wadanda aka kashe a wani tashin hankali da aka yi a jiya (Asabar).

Kakakin gwamnatin Jihar Filato, Mista Pam Ayuba ya tabbatar wa BBC mutuwar 'yan siyasar wadanda 'yan kabilar Berom ne dake fada da kabilar Fulani.

To sai dai kuma ba yi wani karn bayani ba.