An bude taron tallafawa Afghanistan

taron Tokyo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Karzai da masu halartar taron Tokyo

An bude wani taro na kasashen duniya a birnin Tokyo don tattauna irin tallafin kudin da za a baiwa kasar Afghanistan a yanzu har zuwa bayan janyewar dakarun kasashen waje dake kasar a shekara ta dubu biyu da goma sha-hudu.

Shugaba Hamid Karzai ya ce duk wani kokarin da za a yi na cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma sasantawa ba zai yi nasara ba muddin ba bu wani taimako daga kasashen waje.

Lokacin da yake magana bayan taron; Ministan harkokin wajen kasar Japan Koichiro Gemba ya ce kasar sa da Jamus sun kuduri aniyar taimakawa kasar ta Afghanistan:

Yace, "A taron na Tokyo, kasashen biyu sun yi niyyar taimakawa kasar ta fuskar siyasa da kudi don samun cigaba ta fuskar mulki da cigaban kasa.

Karin bayani