Malaman zabe sun yaba da futowar jamaa a zaben Libya

zabe a Libya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption wata na kada kuria a Libya

Malaman zabe a kasar Libya sun ce kimanin kashi sittin cikin dari na mutanen da suka cancanci kada kuri'a sun yi zabe a ranar Asabar.

Zaben shine karon farko na kasar da aka gudanar cikin kusan rabin karni.

'Yan takara a zaben suna neman kujerun majalisar dokoki ne wadda za ta maye gurbin gwamnatin wucin-gadi da aka kafa bayan hambarad da Kanar Ghaddafi.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague ya ce mutanen kasar ta Libya sun yi wani yunkuri na tarihi na samun 'yancin kai da kafa gwamnatin da za ta rinka bayanin al'amurra ga jama'ar ta.

Karin bayani