Dubban mutane na zanga zanga a Mexico

shugaban kasar Mexico Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Caldero da Lula

Dubban mutane a birnin Mexico sun yi boren nuna rashin amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa da aka yi mako guda da ya wuce wanda Enrique Pena Nieto ya samu nasara.

Masu boren da suka kunshi manyan kungiyoyi da suka hada da na 'yan kasuwa da dalibai sun zargi jam'iyyar Pena Neito PRI da laifin sayen kuri'u, zargin da Jamiyyar ta musanta.

Sun rinka waka suna cewa "mexico ba tare da PRI ba", sun kuma rike alluna wadanda a jiki aka rubuta "magudi".

Dan takarar da ya zo na biyu a zaben Andres Manuel Lopez Obrador ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu.

Karin bayani