An kashe mutane 30 a rana guda a Afghanistan

Image caption Shugaba Hamid Karzai

Mutane a kalla talatin aka kashe a rana daya a rikicin da ya faru a sassa daban-daban na kasar Afghanistan.

Wani bam da aka dana gefen hanya a gabashin kasar ya kashe sojojin Amurka shida, wani sojan na kungiyar NATO kuma ya mutu a wani harin da aka kai gabanin wancan.

'Yan sanda da farar hula da dama sun rasa rayukansu wadanda suka hada da wasu mutanen Kauyuka su goma sha takwas a wasu hare-haren na daban da aka kai a kudancin kasar.

Tashin hankalin ya faru ne a yayinda kasashen duniya suka yi alkawarin bayar da dala biliyan goma sha-shida a matsayin taimako ga Afghanistan a wani taro da aka gudanar a birnin Tokyo.

Karin bayani