An sanya dokar hana zirga-zirga a Jos

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Hukumomi a Najeriya sun kafa dokar hana zirga-zirga a jihar Plateau daga karfe shida na yamma zuwa karfe goma sha biyu na rana a kowacce rana.

An sanya dokar ne bayan wadansu 'yan siyasa biyu sun mutu a wani hari da 'yan bindiga suka kai wa taron mutanen da ke binne mutanen da aka kashe a wani wuri kusa da tsakiyar birnin Jos.

Jami'ai sun ce wani Sanata da wani babban dan siyasa na yankin sun mutu daga abin da suka kira firgita a lokacin da ake zargin makiyaya Fulani suka bude wuta.

Wani wakilin BBC a Najeriya ya ce mai yiwuwa harin ramuwar gayya ce ga kisan da jami'an tsaro suka yi wa fiye da Fulani ashirin bayan sun kai hari a kan kauyukan.

Karin bayani