Sojin Masar na shawarwari a kan dawo da Majalisar Dokoki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Masar Mohammed Mursi

Hukumomin Soji da na fannin shari'a a kasar Masar suna wasu shawarwarin gaggawa bayan sabon zababben shugaban kasa, Mohammed Morsi, ya umurci Majalisar Dokokin kasar ta koma zama.

A ranar Litinin ne Kotun Tsarin Mulkin kasar wadda ta rusa Majalisar Dokokin a watan jiya za ta zauna don tattauna wa a kan hanyar da za ta mayar da martani ga umarnin da Shugaba Morsi ya yi.

Majalisar Koli ta sojojin kasar wadda ke rike da ikon da Majalisar Dokokin kasar take da shi ta gana a wani zaman gaggawa jim kadan bayan shugaban kasar ya zartar da ikonsa.

'Yan Majalisar Kolin ta soji suna shirin wani zaman saboda a zaman farko da suka yi ba a cimma matsaya ba.

Karin bayani