Uwargidan Marigayi Arafat za ta yi kara kan mutuwarsa

Marigayi Yasser Arafat da matarsa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Marigayi Yasser Arafat da matarsa

Lauyoyin uwargidan, marigayi Yasser Arafat ta ce za ta shigar da kara a Faransa dan ta nemi mahukuntan kasar su gudanar da bincike kan mutuwarsa, bayan wani shirin talabijin da aka nuna inda akai zargin cewa an bashi guba ne.

A ranar litinin ne shugabannin Palasdinawa suka amince da a tono gawarsa, suka kuma nemi da a gudanar da bincike kan mutuwar tasa a asibitin sojoji na kasar ta Faransa a shekara ta 2004.

A makon da ya gabata ne dai gidan talabijin na Aljazira ya bayyana bayanin wani bincike da ya gudanar, wanda ke nuna cewa an kashe shi ne da gubar sinadarin polonium.

Karin bayani