Birtaniya za ta gurfanar da mutane uku kan taaddanci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan sanda a Birtaniya

'Yan Sanda a Birtaniya sun ce an tuhumi wasu mutane uku da suka fito daga birnin Birmingham da laifuka na ta'addanci kuma nan gaba kadan a yau Talata za a gurfanar da su gaban Kotu.

Mutanen da shekarunsu suka kama daga ashirin da uku zuwa da bakwai, an zarge su ne da makarkashiyar aikata ta'addanci.

Mutanen uku an kuma zarge su da kerawa ko kuma harhada wasu nakiyoyi da bindigogi da abubuwan hawa dangane da shirin su na aikata ta'addancin.

Hukumar dake tuhuma da gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata wasu laifuka ta Birtaniya ba ta yi wani sharhi ba a kan ko akwai wani wuri takamaimai da suke shirin kai harin.

Karin bayani