'Yan tawayen Congo na kutsawa gabacin kasar

Jamian tsaro a Congo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jamian tsaro a Congo suna rangadi

Gwamnatin Jamhuriyar Democradiyyar Congo ta bayyana kaduwar ta da kara dannawar da 'yan tawaye ke yi suna neman isa Goma - babban birnin dake yankin gabashin kasar.

Mutanen da suka shaida lamarin sun ce ga alama ba su fuskanci wata kwakkwarar turjiya wajen kwatar garuruwa da Kauyuka ba kuma yanzu haka tazararsu ba ta kai kilomita arba'in ba.

Goma babbar cibiyar kasuwanci ce wadda ta yi iyaka tsakanin kasashen Congo da Rwanda.

Gwamnatin Congo da Majalisar Dinkin Duniya sun ce Rwanda ce ke mara wa 'yan tawayen baya.Rwandar ta musanta haka.

Congon ta zargi makwabciyar ta da kokarin kawo rashin zaman lafiya, ta yadda za ta rinka dibar albarkatun kasar ta.

Karin bayani