An yankewa Lubanga hukuncin daurin shekaru 14

Thomas Lubanga Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tsohon madugun mayakan sa-kai na Congo, Thomas Lubanga

Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC) ta yankewa tsohon jagoran mayakan sa-kai na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, Thomas Lubanga, hukuncin daurin shekaru goma sha hudu a gidan kaso.

A watan Maris ne dai kotun ta samu Mista Lubanga da laifin yin amfani da yara kanana a kungiyar mayakan sa-kai ta Union of Congolese Patriots (UPC) yayin yakin da aka fafata a yankin Ituri na gabashin kasar Congo daga shekarar 2002 zuwa 2003.

Akalla mutane dubu hamsin aka kashe a rikicin kabilancin da aka tafka a lokacin tsakanin kungiyar ta UPC mai wakiltar 'yan kabilar Hema da 'yan bindiga daga al'ummar Lendu.

Alkalin da ya shugabanci zaman Kotun, Adrian Fulford, ne ya karanta hukuncin:

“Idan aka samu mutum da aikata laifi fiye da daya, to kotu za ta ayyana hukunci a kan ko wanne laifi da kuma hukunci na bai-daya wanda ke fayyace jumlar shekarun da zai yi a gidan kaso”, in ji Alkali Fulford, wanda ya kara da cewa, “Don haka, idan muka yi la'akari da dukkan batutuwan da muka tattauna, mafi rinjayen alkalai sun tafi a kan yankewa Mista Lubanga hukuncin daurin shekaru goma sha uku saboda aikata laifi na farko da hadin gwiwar wadansu mutane, wato tilasta yara ’yan kasa da shekaru goma sha biyar shiga cikin kungiyar UPC.

“Dangane da laifin da ya aikata da hadin gwiwar wadansu mutane na sanya yara ’yan kasa da shekaru goma sha biyar cikin mambobin kungiyar UPC kuma, an yanke masa daurin shekaru goma sha biyu; sannan saboda samunsa da aikata laifi na uku da hadin gwiwar wadansu mutane, wato amfani da yara ’yan kasa da shekaru goma sha biyar a yaki, an yanke masa hukuncin shekaru goma sha biyar.

“Don haka a bisa tanadin Sashe na 783, an yankewa Mista Lubanga hukuncin daurin jimillar shekaru goma sha hudu”.

Masu shigar da kara dai sun bukaci a yankewa Thomas Lubanga hukuncin shekaru talatin ne; amma zaman kason da zai yi na rabin abin suka nema ne, saboda za a debe shekaru shidan da ya kwashe a tsare a hannun kotun ta ICC daga hukuncin nasa.

Kotun ta yi hakan ne saboda Alkali Adrian Fulford ya yaba da kyawawan halayen da tsohon jagoran mayakan sa kan ya nuna da kuma hadin kan da ya baiwa kotun.

Amma dai alkalin ya yi kakkausar suka a kan halayen da tsohon mai shigar da kara na kotun, Luis Moreno Ocampo, ya nuna.

Alkalin ya zargi Mista Ocampo da tafka kurakurai, da gazawa wajen mika hujjojin da ke karfafa ikirarin da ya yi, da kuma kyale ma'aikatansa su rika baiwa ’yan jarida bayanai masu cin karo da juna.

Mista Lubanga ne dai mutum na farko da kotun ta ICC ta yankewa hukunci saboda samunsa da ta yi da aikata laifuffukan yaki.

A da dai Mista Lubanga kwamanda ne a kungiyar 'yan tawaye ta RCD-ML mai samun goyon bayan Uganda, amma bayan an mayar da shi saniyar-ware sai ya balle ya kafa kungiyar UPC.

Mista Lubanga, wanda yanzu yake da shekaru hamsin da daya da haihuwa, ya yi karatu a Jami'ar Kisingani, yana kuma da mata da ’ya’ya bakwai.

An fara kama shi ne a shekarar 2005 aka tsare shi a wani otal da ke birnin Kinshasa; shekara guda bayan nan kuma ya zubar da hawaye lokacin da aka dauke shi a jirgin sama zuwa birnin Hague.

Karin bayani