Dambarwar ikon mulki ta kunno kai a Masar

Mursi da Tantawi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Mursi da Tantawi na karbar fareti

Dambarwa ta kunno kai tsakanin Shugaban kasar Masar da kuma Sojin kasar inda suke ja inja kan umarnin da Shugaba Mursi ya bayar cewa majalisa ta dawo bakin aiki.

Ita kuwa majalisar Koli ta sojoji a kasar Masar ta ce dole ne a yi aiki da tanade-tanaden tsarin mulkin kasar, bayan sabon Shugaban kasar ya yi fatali da shawarar da majalisar sojojin ta zartar ta rusa majalisar dokokin kasar.

A bisa umurnin Shugaba Morsi, Shugaban majalisar dokokin kasar ya kira taron wakilan majalisar a yau talata.

To amma a cikin wata sanarwa, majalisar koli ta sojojin ta ce, rusa majalisar dokokin da ta yi, ta aiwatar da hukuncin kotun tsarin mulkin kasar ne, don haka lallai ne kowane mahaluki ya yi aiki da wannan hukunci.

Tun farko Kotun tsarin mulkin ta bayyana cewar hukuncin ta wajibi ne a yi aiki da shi, ba a kuma iya daukaka kara.

Karin bayani