Birtaniya ta kasa yin gyara ga majalisar dattawa

Majalisar Dattawa Burtaniya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Majalisar dattawan Burtaniya ta cika makil

Gwamnatin hadaka ta Birtaniya ta jingine shirinta na yin gyaran fuska ga majalisar dattijawan kasar, saboda adawar da 'yan majalisar da ke goyon bayanta suka nuna.

Kashi 90% ne na wakilan majalisar dake cikin gwamnatin hadakar suka kada kuriar kin amincewa da kudurin dokar.

Jam'iyyar adawa ta Lebour dai ce kawai ta baiwa kudurin goyon bayan da ya sa za a iya cigaba da tattaunawa a kansa.

Kudurin dokar ya kunshi cewa 'yan majalisar dattawan kasar su ma a rika zabarsu, maimakon gadon kujerun majalisar ko kuma nada su, kamar yadda yake halin yanzu.

Matakin dai, na daya daga cikin manyan manufofin jamiyyar dake cikin gwmanatin hadakar wato Liberal Democrats.