'Yan gudun hijira 54 sun hallaka a tekun Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Hukumar Kula da 'Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wasu mutane 54 sun mutu a lokacinda su ke kokarin zuwa kasar Italiya daga Libya ta teku, a wani dan karamin kwale kwale da ake hura ma Iska.

Mutum daya tilo da ya tsira da ransa daga cikin mutanen dake cikin jirgin ya ce wadanda suka mutun sun rasu ne sakamakon rashin ruwa a jikinsu tsawon kwanaki 15 da suka yi a tekun.

Ya shedawa hukumar kula da 'yan gudun hijirarar cewa har sun kusa zuwa gabar tekun Italiya amma wani iska mai karfin gaske ya sake tura su baya, daga nan sai iskan kwale kwalen nasu ya fara sacewa.

Masu kamun kifi ne suka cece shi a gabar ruwan Tunisia kuma ana jin galibin mutanen da ke cikin kwale kwalen sun fito ne daga Eritrea

Karin bayani