Gwamnatin Nijeriya ta amince da dokar mai

matsalar malalar mai a yankin Niger Delta Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption matsalar malalar mai a yankin Niger Delta

A Najeriya, majalisar zartarwar kasar ta amince da wani sabon kudirin doka a kan harkokin mai.

Ana sa ran dai za a mika wa majalisar dokokin kasar wannan kudurin doka nan ba da dadewa ba.

Sabon kudirin dokar ya fito da wasu sababbin sauye-sauye, wadanda gwamnatin Najeriyar ta ce zasu taimaka wajen bai wa 'yan kasar damar shiga a dama da su a harkokin haka da kuma kasuwancin mai.

A wata hira da BBC, ministan yada labaru na Nijeriya , Mr Labaran Maku ya ce wannan sabuwar doka zata share fagen karuwar saka-jari na kasashen waje a Nijeriya, za kuma ta bada 'yan kasa damar shiga a dama da su a harkar mai, fiye da irin rawar da suke takawa a al'amarin a yanzu.

Karin bayani