Jakadan Syria a Iraki ya sauya sheka

Kofi Annan, mai shiga tsakani a Syria Hakkin mallakar hoto s
Image caption Kofi Annan, mai shiga tsakani a Syria

An bayar da rahoton cewar Jakadan Syria a Iraqi, Nawaz Fares, ya sauya sheka.

Idan hakan ya tabbata zai kasance babban jami'in diplomasiya na farko da ya dawo daga rakiyar gwamnatin Shugaba Bashar Al-Assad.

An nada Nawaz Fares a matsayin jakada zuwa Bagadaza ne a 2008.

Shi ne jakadan Syria na farko a Iraqi a cikin shekaru 30, saboda rashin kyaun dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Shi dai ya kasance mai goyon bayan jama'iyar Ba'ath ne, kuma tsohon Gwamna a larduna da yawa.

Rahoton dai ya zo ne mako guda kawai bayan da wani babban hafsan soji, ministan tsaron kasar da ya fi dadewa , ya sauya sheka.

A halin da ake ciki, kasashen Yammacin duniya a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na barazanar daura karin takunkumi a kan gwamnatin Syriar, idan ba ta kawo karshen hare haren da take kai wa a kan 'yan kasarta ba.

Karin bayani